• Breaking News

    Hagia Sophia

    Hagia Sophia a Halin yanzu


     Hagia Sophia

    Harshen Turkanci Ayasofya, harshen Latin Sancta Sophia , ana kuma kiran ta da Church of the Holy Wisdom ko Church of the Divine Wisdom, gini ne da yake a birnin Istanbul, Turkiyya, an gina shi tun a karni na 6 kafin haihuwar annabi Isah (a.s) tsakanin shekarun (532–537) a karkashin jahorancin shugaban daular Byzantine Justinian I. Wannan gini shine gini mafi muhimmanci a daular Byzantine kuma daya daga cikin kayaiyakin da hukumar dake taskance muhimman abubuwan tarihi ta duniya UNESCO ta saka shi a jerin ta. Asalin ginin an yishi ne a matsayin coci wanda al'umar kiristoci ke halarta domin ibada.

    Ana kallon masallacin a matsayin gini mafi girma a duniya.
    Ya kasance a hannun mulkin masarautar Byzanite kafin shekara ta 1204 da aka ci birni a yaki.

    MAYAR DA HAGIA SOPHIA MASALLACI

    Sakamakon cigaba da yaduwar da addinin musulunci yakeyi a yankin gabas ta tsakiya a wancan zamanin ne har takaiga musulmai sun kwace baki dayan yankin na Turkiyya a yanzu tare da kafa hadaddiyar daular nan mai girma ta musulunci ko daular Usmaniyya ko Ottomon ne yasa gaba daya yankin yakoma a tsarin Musulunci.
    Daular Usmaniyya ta Ottoman Sulta Mehmed II ta kwace birnin Istanbul (wanda a baya ake kiran shi da suna Constantinople) kuma ta yi nasara jagorantar sallar juma'a ta farko a wurin bautar wato Hagie Sophia.
    Masarautar Ottoman ta mayar da ginin baki daya masallaci, sannan ta sauya abin da aka lulube gini da kuma sauya rubutun da ke jikinsa zuwa na Musulunci.

    MAYAR DA HAGIA SOPHIA GIDAN TARIHI

    Bayan kwashe shekaru mai tarin yawa a karkashin daular Ottoman, a shekarar 1934 aka mayar da ginin wurin zuwa yawon bude ido a wani kokari na mayar da Turkiyya kasa mai zaman kanta da soke bangaranci.
    Kemal Ataturk, mutumin da shine ya assasa kasar Turkiyya zuwa zamani kuma kasa wadda ba ruwan ta da tsarin addini ya kagoranci mayar da Hagia Sophia zuwa Gidan tarihi.
    Hakan yajawo hargitsi daban daban daga masu kishin Islama da musulman kasar dama musilman sassan duniya da dama.
    Gidan tarihin na Hagia Sophia ya kasance fitaccen wurin yawon bude ido a Turkiyya da duk wanda ya je kasar ke burin ziyarta, akalla mutum miliyan 3.7 ke ziyarta ginin a kowacce shekara.
    An kwashe tsawon shekara tamanin Hagia Sophia na a matsayin gidan tarihi.

    MAYAR DA HAGIA SOPHIA ZUWA MASALLACI KARO NA BIYU

    Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ma komawar Hagia Sophia zuwa masallaci a watan Yuni na 2020.
    Wannan hikuncin yazo ne albarkacin gwagwarmayar da ƙkungiyoyin Turkawa masu kishin addinin Musulunci suka shafe tsawon shekaru gommai suna yi da kuma burin Shugaba Erdogan, Hagia Sofia ta sake zama masallaci.
    Ranar juma'a 24 Yuli, 2020 aka yi sallah karon farko a masallacin tun bayan shafe shekaru tamanin a matsayin gidan yarihi.
    Al'umar kasar sun matukar nuna farin cikin su a titunan kasar dama kafafen sada zuminci.
    Saidai wasu al'umar kasar musamman ma mabiya addinin kirista hukuncin baiyi masu dadi ba.
    Amma al'umar musulmai da dama daga sassan duniya sunyi murna da mayar da Hagia Sophia ziwa masallaci. Amma kuma akwai bangarorin da suka mayar da martani na nuna rashin jin dadi da lamarin. Paparoma shugaban darikar katolika na duniya ya nuna rashin jin dadinsa. Hakama hukimar adana kayan tarihi ta duniya UNESCO bata ji dadin lamarin ba.
    Saidai cikin rashin razana, shugaba Erdogan yayi kausasan martani ga masau sukar lamirin nasa.
    Wasu na kallon lamarin da shugaba Erdogan ya dauka na mayar da gidan tarihin zuwa masallaci a matsayin wata alama da Erdogan ke nuna ma duniya da cewar yana son ya zama babban mai fada a ji kima jagora ga al'umar musulman duniya.
    rubutawa da sharhi daga Abubakar A Gwanki, kana iya baiyana ra'ayinka a akwatun sharhi dake kasa

    No comments